Za a sake shari'ar Mubarak a Masar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Za a sake shari'ar tsohon shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak.

Za a sake shari'ar tsohon shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak a kotu bisa zarginsa da hannu wurin kashe darururwan 'yan zanga-zanga lokacin boren da aka yi ma sa a shekarar 2011.

A bara kotu ta yi watsi da zargin saboda rashin kwakkwarar shaidu, amma masu shigar da karar sun daukaka kara a kotu.

Babbar kotun Masar ta karbi karar a don haka za a sake shari'ar.

Asali an yanke wa Mr. Mubarak hukuncin daurin rai da rai a kan laifin, amma sai aka wanke shi.

Wannan shi ne zama na karshe da kotu za ta yi a kan zargin, kuma baza a sake wata zama ba domin daukaka karar.