Ana mahawara kan aure a Twitter

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An tsaurara rabewa tsakanin mata da maza a Saudiyya.

'Yan Saudiyya suna ta tafka muhawara a Intanet a kan wani batu mai sarkakakiya da aka wallafa a shafin Twitter wanda ya bude fagen jayayya tsakanin jinsin maza da mata.

Tun bayan da aka wallafa "Kar ku auri dan Saudiyya", jama'a suke ta tsokaci tare da barkwanci.

Wasu matan sun ce basu da niyyar auren dan Saudiyya, a kasar da har yanzu mata suka dogara ga namiji a matsayin waliyi.

Wasu mazan da mata kuma sun kare mazan ne 'yan Saudiyya da cewa su ne suka san martabar kare al'adun su.

A Saudiyyar dai ana tsaurara rabewa tsakanin jinsin maza da mata amma suna musayar ra'ayi ta hanyar Intanet ba tare da wani shamaki ba.