Sheriff ya mika kansa ga EFCC

Hakkin mallakar hoto Modu Sheriff Twitter
Image caption Sheriff ya shafe shekaru takwas a matsayin gwamnan jihar Borno

Tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff ya mika kansa ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa, EFCC.

Sheriff ya mika kansa ga EFCC ne a ranar Laraba bisa zarginsa da ake yi da cin hanci da karbar rashawa.

Mr Wilson Uwujaren, mai magana da yawun hukumar EFCC ya ce "tsohon gwamnan ya zo ofishinmu jiya (Laraba) da yamma kuma sai da karfe goma na dare ya bar ofishinmu."

Duk da dai cewa har yanzu ba a san laifukan da EFCC ta ke tuhumar tsohon gwamnan da shi ba, wasu majiyoyin sun ce bincike da ake yi ya danganci tuhumar zargin sama da fadi da dukiyar al'umma.

An fara binciken ne tun a 2012 kuma har yanzu ba a gabatar da Sheriff gaban kuliya ba.