Kungiyar IS ta fille kawunan 'yan Taliban

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Taliban ba sa ga maciji da mayakan IS

Dakarun Afghanistan sun ce mayakan kungiyar IS sun fille kawunan wasu 'yan Taliban su 10 a yankin gabashin kasar.

Ana hasashen cewa wannan ne karon farko da aka hallaka mayakan Taliban ta wannan hanyar.

An samu bayanan kisan ke a wata wasika ta sirri da aka aika wa manema labarai bisa kuskure.

Fille kawunan 'yan Taliban din na zuwa ne bayan makonni da aka shafe ana fafatawa tsakanin kungiyoyin biyu a lardin Achin da ke kusa da kan iyaka da kasar Pakistan.

A waje daya kuma Amurka ta ce an hallaka mayakan IS 10,000 tun lokacin da sojojin kawancen kasashe suka soma fafatawa da 'yan IS a kasashen Iraki da Syria.