Gambia ta kori wakiliyar Tarayyar Turai

Image caption Gambia na yaki da masu aikata luwadi

Gwamnatin Gambia ta kori wakiliyar kungiyar Tarayyar Turai EU Agnès Guillaud daga kasar.

An dai bata sa'oi 72 data tattara inata- inata ta bar kasar.

Babu dai wani dalili da gwamnatin Gambian ta bayar na daukar wannan mataki .

Sai dai Kungiyar Tarayyar Turai na sukar yadda Gwamnatin Gambian ke tunkarar batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam, kuma ko a bara Kungiyar ta hana wani tallafi na dala miliyan 15 ga Gambian.

Sukar da kungiyar EUn ke yiwa Gambian dai, yafi karkata ne kai tsaye ga dokokin Gambian na haramta yin luwadi