Nestle zai janye taliyarsa daga kasuwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamfanin Nestle ya ce taliyarsa lafiya lau take amma ya ce yana la'akari ne da koke koken jama'a

Kamfanin Nestle ya ce zai janye wata Taliya mai farin jini daga kasuwannin kasar Indiya, saboda tsoron cutar da lafiyar jama'a.

Jihohi da dama sun hana cin taliyar ta Maggi instant noodles, bayan gwaje-gwajen da aka yi, wanda ya nuna cewa Taliyar na dauke da dalma mai yawa a cikinta.

Kamfanin Nestle na Indiya ya ce ya yi imanin taliyar bada da hatsari, amma ya dau wannan matakin ne, domin abinda ya kira rudanin da Kwastomomi suka shiga.

Kamfanin ya ce zai koma sayar da taliyar da zarar an magance wannan damuwar data taso.

Kashi 80 cikin 100 na kasuwar abinci a Indiya, na dauke da Taliyar Maggi noodles.