"Afrika na bukatar inganta lantarki"

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tsohon shugaban Majalisar Dinkin Duniya Mista Kofi Annan

Tsohon shugaban Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan, ya yi kira da a samar da asusun tallafi na biliyoyin daloli domin ya taimaka wajen samar da tsaftataccen makamashi a nahiyar Afrika.

Mista Annan, wanda ya jagoranci kwamitin ci gaban Afrika, ya ce kamata ya yi kasashen Afrika su dinga amfani da kudaden da suke batarwa wajen tallafin man fetur domin samar da wutar lantarki.

Mista Annan ya gaya wa BBC cewa za a iya cimma wannan manufa cikin shekaru 15 da taimakon kasashen duniya.

Ya kuma fitar da wani sabon rahoto gabannin taron sauyin yanayi na duniya da za a yi a karshen shekarar nan a birnin Paris.