Jam'iyyar adawar Nijar za ta bi sahun APC

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zaben Muhammadu Buhari ya zama abin koyi daga wasu kasashe makwabta

Jam'iyyar adawa ta CDS Rahama da ke Jamhuriyar Nijar ta fara wani yunkuri na neman hada kai da jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

A wannan mako ne dai wasu shugabannin jam'iyyar ta CDS Rahma suka ziyarci shugabannin jam'iyyar APC a Najeriya a wani mataki na ganin sun kulla kawance tare da daukar darasi daga jam'iyyar APC.

Alhaji Dudu Rahma, wanda shi ne Kakakin Jam'iyyar CDS Rahma ya shaidawa BBC cewa, sun sami saduwa da manyan 'yan siyasar Najeriya da suka nuna jajircewa har suka kai ga nasara.

Ya ce sun koyi darasin daga irin yadda 'yan sisayar Najeriyar suka jure goyan bayan zababben Shugaban Kasar Muhammadu Buhai tsawon shekara da shekaru.