Tariq Aziz ya rasu a kurkuku a Iraki

Image caption Margayi Tariq Aziz

Rahotanni daga Iraki na cewa Allah Ya yi ma Tariq Aziz tsohon ministan harkokin wajen Iraki rasuwa.

Tariq Aziz makusanci ne ga tsohon shugaban kasar Saddam Hussein.

Ma'aikatar shari'a ta Iraki ta ce Tariq Aziz ya rasu ne a kurkuku.

Aziz mai shekaru 79, ya kasance ministan harkokin waje kuma mataimakin Firaminista a gwamnatin Saddam.

A shekara ta 2010 ne aka yanke masa hukuncin kisa saboda irin rawar da ya taka a zamanin mulkin Saddam Hussein.