An bukaci Buhari ya taka wa sojoji birki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Buhari ya yi alkawarin magance matsalar Boko Haram

Babban jami'in kula da hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya, ya yi kira ga sabon Shugaban Najeriya, da ya binciki cin zarafin da ake zargin dakarun sojin kasarsa da shi a yaki da Boko Haram.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ta yi zargin cewa mutane sama da 8,000 ne suka mutu kulle a gidajen yarin sojojin.

Jami'in Majalisar Dinkin Duniya, Zeid Ra'ad Al-Hussein, ya yi Allah wadai da mummunar aikin zaluncin Boko Haram ke aikatawa.

Jami'an Najeriya sun ce an kashe akalla mutane 38 a sakamakon fashewar bam a garin Yola, da ke Adamawa da yammacin ranar Alhamis.

Wannan wani sabon hari ne da ake zargin kungiyar Boko Haram ce ta kaddamar.