An yi wa ma'aikatan Amurka miliyan 4 kutse

Hakkin mallakar hoto
Image caption Masu amfani da kwamfuta a Amurka

Hukumar binciken laifuka ta kasar Amurka FBI ta na gudanar da binciken yadda masu satar bayanai a kwamfuta suka yi nasarar kutse a bayanan sirri na ma'aikatan gwamnatin kasar su miliyan 4.

Hukumar dake kula da harkokin ma'aikata a kasar ta bayyana lamarin a matsayin babban kutse.

A sakamakon kutsen wanda aka gano a watan Afrilu, hukumar kula da harkokin ma'aikatan a Amurka ta ce za ta sanar da kimanin ma'aikata miliyan hudu da lamarin ya shafa.

Hukumar ta ce tana kokarin cimma dukkan ma'aikatan da suka hada da tsofaffi domin kare su daga sharrin masu damfara da sunan su.

Babu dai masaniya ko cikin ma'aikatan da kusten ya shafa har da shugaba Obama da wasu manyan jami'an gwamnati, ko kuma hukumomin leken asisrin kasar.

Jaridar Washington Post da wasu kafafen yada labarai a Amurka sun ambato wasu jami'an gwamnati suna zargin masu satar bayanai a kwamfuta 'yan kasar China da laifin.

Sai dai ofishin jakadancin China a Washington ya yi watsi da zargin da wasu jami'ai a Amurkan su kayi cewa daga China kusten ya yo asali.

Wannan shi ne kuste na baya bayan nan da kasar da fuskanta, wanda ke bayyana raunin gwamnatin tarayyar kasar.

A bara, an yi amanna wasu masu kuste 'yan kasar Rasha sun samu damar satar wasu muhimman bayanan fadar shugaban kasar White House da kuma na ma'aikakar harkokin wajen kasar.

A wancan lokaci masu satar bayanan sun saci bayanan masu biyan haraji kimanin dubu 100.

Shugaba Obama dai ya bayyana China da Rasha a matsayin na gaba gaba a harkar satar bayanai ta intanet, inda ya ce Iran ke bi masu, sannan kasar korea ta arewa.