Dubban mutane sun yi zanga-zanga a Nijer

Hakkin mallakar hoto AFP

Dubban mutane sun yi zanga-zangar lumana a Yamai, babban birnin Nijer.

Sun ce suna nuna adawa ne da karancin wutar lantarki da shirin kara yawan 'yan majalisar dokoki da kuma sauran matsalolin da suka ce sun addabi kasar.

Kimanin kungiyoyin fararen hula 40 ne suka shirya zanga-zangar wadda aka yi a ranar Asabar.

Masu zanga-zangar sun kuma zargi gwamnati da rashin yin aiki tukuru domin magance matsalar Boko Haram a kudancin kasar.

Amma jami'an jami'iyyar da ke mulkin kasar sun yi watsi da zarge-zargen, suna nuni da cewa 'yan adawa ne suka shirya zanga-zangar domin bata wa gwamnatin suna.

Karin bayani