Saudiyya ta harbo makamin Scud na Houthi

Hakkin mallakar hoto Reuters

Hukumomin Saudiyyar sun ce sun kakkabo makamin mai linzami ne a daren ranar Juma'a.

Suka ce an harba makamin ne zuwa birnin Khamees Mushait.

Sun kuma baiyana harba makamin mai linzami a matsayin wata sabuwar tsokanar fada dangane da rikicin na Yemen.

A baya bayan nan dai Saudiyar ta zafafa hare haren da ta ke jagoranta ta sama a kan 'yan Houthin.

Wannan na faruwa ne gabanin tattaunawar sulhu da za'a yi a Switzerland wanda Majalisar Dinkin Duniya ke fatan za'a fara a mako mai zuwa.

Bangarorin biyu dai sun ce za su halarta.