BBC ta gano cewa Warner ya shaki daloli

Hakkin mallakar hoto warner tv
Image caption Sabbin bayanai sun nuna cewa Jack Warner na da hannu dumu- dumu a cin hancin da ya dabaibaye FIFA

Wani binciken da BBC ta gudanar ya bankado abinda ya faru ga dala miliyan 10 da aka tura daga asusun FIFA zuwa wani asusu wanda ke karkashin ikon tsohon mataimakin shugaban hukumar FIFA Jack Warner.

Afirka ta Kudu ta saka kudaden ne da nufin bunkasa harkar wasan kwallon kafa a yankin Caribbean tun farko

Amma bayanai da BBC ta gani, sun nuna cewa Mr Warner ya yi amfani da asusun domin fitarda kudade, da kuma bai wa kansa bashi daga ciki, da kuma halarta kudaden haram

Hukumar FBI dai na bincikar wannan badakala wacce ita ce mafi muni data dabaibaye hukumar kwallon kafa ta FIFA

Jack Warner dai ya musanta cewa ya yi wani abu ba dai-dai ba.