Ana rikicin shugabancin majalisar dokoki

Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption Kawunan 'yan majalisar dokokin Nigeria ya rabu yayinda ake tunkarar zaben Shugabannin majalisun

A Najeriya jam'iyyar APC mai mulki ta fidda Sanata Ahmed Lawal daga jihar Yobe a matsayin wanda take so ya zama shugaban majalisar dattijai, yayin da Sanata George Akume daga jihar Benue zai yi masa mataimaki.

Jamiyyar APC ta fidda wadannan 'yan takara ne a wani zabe na share fage da ta shirya a daren ranar Asabar

Sai dai, wasu 'yan majalisar dattawan su 65 karkashin jam'iyyar da ake gani suna marawa Sanata Bukola Saraki baya, basu halarci taron ba

Kuma sun ce lallai sai dai uwar jam'iyyar ta bar 'yan majalisar su zabi Shugabannin su a ranar Talata.

A majalisar wakilai ma

An samu wani rudanin a shirin da shugabannin jam'iyyar APC na kasa suka yi , domin tsaida mutanen da zasu yi takarar shugabancin majalisar wakilan kasar.

Hon. Femi Gbajabiamila daga jihar Lagos da kuma Yakubu Dogaro ne ke neman kujerar kakakin majalisar.

Sai dai shugabannin jam'iyyar APC sun tsaida Femi Gbajabiamila daga jihar Lagos a zaben da aka gudanar na share fage, a matsayin wanda zai yi takarar Kakakin majalisar wakilan.

To amma magoya bayan Yakubu Dogara sun ce basu amince da wannan zabe ba, har ma suka fice daga taron a lokacin da ake yin sa.

Tuni dai wasu ke ganin wannan lamari ka iya kawo rarrabuwar kanuwa a cikin jam'iyar ta APC tun ba je ko' ina ba.