Buhari ya gana da shugabannin G7

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Buhari a Jamus tare da shugabannin G7

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin manyan kasashe masu ci gaban tattalin arziki na duniya G7 a taron da suke gudanarwa a Jamus.

Shugabannin sun gaiyaci shugaban Najeriyar ne domin ya gabatar da jadawalin bukatun da kasarsa ke son a tallafa mata kansu.

Mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya shaidawa BBC cewa batutuwa da suka shafi tsaro da cin hanci da rashawa da kuma zuba jari su ne shugaban kasar ya gabatarwa da shugabannin.

A waje daya kuma, shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta bayyana karara cewar a shirye kungiyar G7 ta ke ta kara tsuke takunkumin da ta saka wa gwamnatin Rasha.

Merkel ta ce "Hadin gwiwar wadannan kasashe bakwai suna Allah-wadai da mamaye Crimea, wanda ya sabawa dokokin kasa-da-kasa."

Shugabannin kungiyar ta G7 dai na yin tattaunawarsu a rana ta biyu, inda matakan magance sauyin yanayi da kuma tsatsauran ra'ayi ke kan gaba a tsarin abubuwan tattaunawar.