An tsayar da ranar zabe a Burundi

Masu zanga-zanga a Burundi
Image caption wasu masu zanga-zangar kyamar ta-zarcen Nkurunziza

Hukumar zaben Burundi ta ce za a yi zaben kasar da ke cike da ce-ce-ku-ce ne cikin tsakiyar watan Yuli.

Da dai ranar ashirin da shida ga watan Yuni aka yi niyyar yin zaben, amma shirin shugaba Pierre Nkurunziza na neman wa'adin mulki na uku ya haddasa tarzoma sosai, da kuma yunkurin juyin mulki da bai kai labari ba.

Kakakin hukumar zaben ya fada wa BBC cewa ranar 26 ga watan Yuni za a yi zaben 'yan majalisar dokoki, yayin da kuma za a yi zaben shugaban kasa ranar 24 ga watan Yuli.

Cikin makon jiya ne dai tsohon sakatare-janar na majalisar dinkin duniya, Kofi Annan ya yi kira ga shugaba Nkurunziza ya sauka daga mukaminsa.