Masar: Al- Sisi ya nemi afuwar lauyoyi

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An ce 'yan sanda a Masar na cin zarafin 'yan kasar

Shugaban Kasar Masar Abdel Fattah al Sisi, ya nemi afuwar lawyoyin kasar, bayan wani dan- sanda ya lakadawa wani Lauya duka da takalmi.

Wannan al'amari ya harzuka Lauyoyin kasar tafiya yajin aiki na kwana guda

A wata sanarwa da ya fitar, Mr Sisi ya nemi afuwa ga Lauyoyin, da kuma sauran Misrawa da 'yan sanda suka ciwa zarafi

Sannan yai kira akan jami'an tsaro dasu fahimci cewa suna mu'amala ne da 'yan-adam wajen gudanar da aikinsu, sai dai Sisin bai gabatar da wani tsari ba domin magance matsalar

Masu fafutuka a Masar sunce 'yan sanda a mafi yawancin lokuta na wuce gona da iri wajen gudanar da aikinsu