An kare taron kolin G7 a Jamus

Hakkin mallakar hoto BPA Germany

Shugabannin kasashe bakwai da suka ci gaba ta fuskar masana'antu, wato G7 sun bayyana aniyarsu ta ganin an wuce matsayin kona mai cikin karnin nan, a kokarin shawo kan sauyin yanayi.

A wata sanarwar karshen taro ta hadin gwiwa a taronsu na Jamus shugabannin sun ce, lokaci yayi da za a kawo karshen alakar tattalin arzikin duniya da samar da hayaki mai dumama yanayi.

Haka nan kuma a cikin sanarwar shugabannin kungiyar ta G7 sunce dole a bar takunkumin da aka saka wa Rasha ya ci gaba da aiki har sai an mutunta tsagaita wuta a gabacin Ukraine yadda ya dace.

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce a shirye kasashen kungiyar G7 din suke su kara tsuke takunkumin idan yanayin ya kama.

A wajen taron kolin, Shugaba Obama yayi magana game da matakan da ake bukata don tinkarar kungiyar IS yadda ya kamata a Iraqi.

Obama ya kuma jaddada muhimmancin tafiya tare da kabilu 'yan Sunni wajen yaki da kungiyar ta IS.

Ya kuma ce, akwai bukatar Turkiyya ma ta tallafa wajen kawo karshen kungiyar ta IS.