An janye taliyar Maggi a gabashin Afrika

Image caption Taliyar da Nestle ke yi na da hadari in ji hukumomi

Katafaren shagon sayar da kaya mafi girma a gabashin Afrika, Nakumatt ya sanar da janye taliyar Maggi noodles daga shagunansa a kasashe biyar.

Nakumatt na da rassa a kasashen Kenya da Uganda da Tanzania da Rwanda da kuma Sudan ta Kudu.

Hakan ya biyo bayan matakin haramta taliyar a Delhi babban birnin India a makon da ya gabata.

Hukumar kula da ingancin abinci ta India bayan gwaje-gwaje ta gano cewa taliyar Maggi noodles da kamfanin Nestle ke yi na da 'hadari ga lafiya'.

Hukumar kare hakkin kwastomomi a Kenya ta bukaci bangarorin gwamnati da abin ya shafa, su daina bari ana shigo da taliyar cikin kasar.