Musulman India sun caccaki Modi

Image caption Wasu al'ummar Musulmi a India

Malaman addinin Musulunci a India sun kaddamar da wani kamfe a fadin kasar domin nuna adawa da shirin gwamnati na mayar da wasan yoga ya zama wajibi a makarantun kasar.

Mambobin cibiyar malaman India, wacce ke ba da shawara a kan harkokin addini sun ce tilastawa yara yin wasan yoga sannan kuma su jinjina wa rana ya sabawa koyarwar addinin Musulunci.

Gwamnatin kasar wacce ke karkashin jagorancin mabiyin addinin Hindu, Nerandra Modi na kokarin karfafa wasan yoga a tsakanin al'ummar kasar.

Masu adawa da shirin sun ce matakin wani bakon abu ne ga mabiya sauran addinai a kasar.

Hukumomi a wasu jihohin India a baya sun haramta ci ko sayar da naman shanu saboda girma dambar a idon mabiya addinin Hindu.