Gasar zaman lafiya a Somalia

Image caption Matasan Somalia a taron zaman lafya, inda suke gasar wake-wake da zane.

Bayan yaki da tarzomar da ta dauki shekara 20 a Somalia, gasar wake-wake da kuma zane sun fara tasiri a Mogadishu babban birnin kasar.

Wata kungiyar matasa da ta hada damaza da mata da basu kai shekaru 30 ba, sun yi gasa a taron wake-wake da zane a kan zaman lafiya.

Wasu daga cikin daruruwan mutanen da suka halarci taron sun fashe da kuka bayan sauraran wakokin kishin kasa da matasan suka rera, yayinda wasu kuma suka mike tsaye suna kada kawunan su cikin farin ciki.

Mutane da dama da suka halarci gasar wacce aka fafata tsakanin 'yan makarant, an bukacesu su nuna hotunan da ke bayyana muhimmancin zaman lafiya.

'Mamaki'

Image caption Yaran Somalia sun bada mamaki a kwarewarsu na zane da rera wakokin kishin kasa.

Abun mamaki sai wani dan makaranta ya zana wasu shahararrun gine-gine a Mogadishu a takardarsa, yayinda wani dan firamare ya zana wata mata 'yan Somalia cikin matsanancin hali a karkashin tutar kasar.

Ministan yada labarai na Somalia, Mohamed Abdi Maareeye shi ya bude taron gasar, kuma ya yi bayanin cewa manufar ta ita ce ta hada kan matasan Somalia da yakin ya saka cikin wani hali, su kawo wani yanayi da zai kara dankon zumunci.

Wata mawakiyar Somalia wacce ta yi fice mai suna Muslima Kasin tana cikin wadanda suka yanke hukunci a gasar domin ba da kyautuka.

Image caption Matasan da sukayi nasara za a basu Akuya su yanka.

Wadanda suka yi nasara a gasar an basu kyautar kayan girki na gargajiya da akuyar da za su yanka su ci dukkaninsu idan sun koma kauyukansu.