Zan yi aiki tare da 'yan majalisa - Buhari

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban majalisar dattijai, David Mark

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai yi aiki kafada da kafada da sababbin shugabannin majalisar dokokin kasar da aka zaba.

A wata sanarwa da mataimakinsa na musamman a kan yada labarai Femi Adesina ya fitar, shugaban ya ce ya so a ce matakan da aka bi wajen zaben sun kasance kamar yadda jam'iyyar APC ta tsara.

Amma duk da haka, a ganinsa, an bi kundin tsarin mulkin kasar ta wata fuskar.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hon Yakubu Dogara

A ranar Talata ne dai aka gudanar da zabukan shugaban majalisar dattijai wanda Sanata Bulokla Saraki ya lashe, da kuma na shugaban majalisar wakilai da Yakubu Dogara ya yi nasara.

Dukkannin shugabannin biyu dai sun kasance a baya 'yan jam'iyyar PDP amma daga bisani suka canja sheka zuwa jam'iyyar APC sakamakon rikicin cikin gida da ya ki ci ya ki cinyewa.