Za a kashe mutane 11 a Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane da dama ne suka mutu a rikicin

Wata kotu a Masar ta tabbatar da hukuncin kisa da aka yankewa mutane 11 da ake zargi da hannu a mummunan rikicin da ya biyo bayan wasan kwallon kafa shekaru uku da suka gabata.

Shari'ar dai ta shafi fadan da aka yi ne tsakanin magoya bayan wasu kulob da ke gaba da juna a filin wasanni na Port Said.

Mutane fiye da 70 ne dai suka mutu yayin tashin hankalin.

'Yan sanda da dama sun fuskanci shari'a dangane da rikicin, amma 'yan sandan basa cikin wadanda aka yankewa hukuncin kisa.

Mutanen da aka yankewa hukuncin kisa yau magoya bayan kulob din Al Masry ne na Port Sa'id, wadanda suka mutu a rikicin magoya bayan kulob din Al Ahly na birnin Alkahira.