Bankin HSBC zai rage ma'aikata 25,000

Image caption HSBC zai rage ma'aikata

Daya daga cikin bankuna mafiya girma a duniya, HSBC ya bayyana shirinsa na tsuke bakin aljihu.

Bankin zai yi tsumin kudade ta hanyoyin da suka hada da rage ma'aikata da suka kai dubu ashirin da biyar a dukkan rassansa da ke fadin duniya.

HSBC zai kuma sayar da bangarorinsa a Brazil da kuma Turkiya, sannan zai rage kaddarorinsa na kusan dala biliyan dari uku da darajarsu za ta iya faduwa.

Wakilin BBC kan harkokin tattalin arziki ya ce wannan mataki ba kawai yana nufin tsuke bakin aljihu ba ne, amma wani mataki ne na karkata harkokin bankin ga wasu sassan duniya inda yake da damar bunkasa harkokinsa.

Yawancin wadanda za su rasa aikinsu dai a Biritaniya suke.