Kotu ta saki wacce ta kashe mijinta a Kano

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption A bara ne Wasila ta sanyawa mijinta shinkafar bera a abinci

Wata babbar kotun jihar Kano da ke zama a karamar hukumar Gezawa, ta sallami wata matashiya Wasila Umar, da aka zarga da kashe mijinta da kuma wasu mutane uku ta hanyar zuba musu shinkafar bera a cikin abinci a watar Maris din bara.

Matakin dai ya biyo bayan bukatar haka da masu shigar da kara suka mikawa kotun, dauke da sa hannun tsohon Kwamishinan shari'a na jihar Barista Maliki Kuliya.

A baya dai, kwamishinan ya shaida wa BBC cewa gwamnati ta yanke hukuncin janye tuhumar da ake wa Wasila ne mai shekaru 14, sabo da karancin shekarun ta.

Lauyan gwamnatin jihar Kano-Barista Lamido Abba Soron-Dinki, shi ne ya gabatar da bukatar a madadin kwamishinan shari'a.

To Sai dai wakilin BBC ya lura cewa babu dangin Wasila a kotun, haka kuma dangin mutanen da aka kashe suma babu wanda ya halarci kotun.