Kai Tsaye: Zaben shugabannin majalisa

Latsa nan domin sabunta shafin

Barkanmu da warhaka da kuma ziyartar shafin BBC Hausa kai tsaye a kan zaben shugabannin majalisar dokokin Nigeria watau majalisar dattijai da kuma ta wakilai.

Sai dai kafa sabuwar majalisar na zuwa ne a yayinda jam'iyyar APC mai mulki wadda kuma ke da mafi rinjayen kujeru a majalisar ke fuskantar tayar-da-jijiyar wuya a cikin gida kan wadanda za su shugabanci majalisar.

  • Za ku iya aiko mana da ra'ayoyinku ta e-mail a hausa@bbc.co.uk ko kuma ta shafin BBC Hausa Facebook, ko ta whatsApp 08092950707 ko ta Twitter a @bbchausa.

Mun gode da kasancewa tare da mu. Sai wani lokacin.

18:00 Ana ci gaba da kada kuri'a domin zaben sabon mataimakin shugaban majalisar wakilai.

17:14 Hon Alhassan Ado Doguwa daga jihar Kano ya gabatar da sunan Hon Tahir Monguno a matsayin wanda yakeso ya zama mataimakin shugaban majalisar wakilai.

17:08 Dan majalisa daga jihar Katsina, Babangida Ibrahim ya gabatar da sunana Hon Sulaiman Yusuf Lasun a matsayin wanda yake so ya zama mataimakin shugaban majalisar wakilai.

17:05 Sai kuma batun wanda zai zama sabon mataimakin shugaban majalisar wakilai.

16:46 An rantsar da Hon Yakubu Dogara a matsayin sabon shugaban majalisar wakilai.

16:40 Alhaji Salisu Maikasuwa akawun majalisa, ya sanar da Hon Yakubu Dogara a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban majalisar wakilai.

Hakkin mallakar hoto NTA

16:25 Hon Femi Gbajabiamila daga jihar Lagos ya samu kuri'u 174 a yayinda Hon Yakubu Dogara daga jihar Bauchi ya samu kuri'u 182 a zaben da suka fafata.

16:05 An kamalla kirga kuri'u a zaben shugaban majalisar wakilai.

15:40 An soma kidaya kuri'u a zaben shugaban majalisar wakilai inda aka fafata tsakanin Gbajabiamila da kuma Yakubu Dogara

14:35 Fiye da rabin zababbun 'yan majalisar wakilai sun kamalla kada kuri'a a zaben shugabansu.

14:20 'Yan majalisa daga jihohin Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue , Borno, Cross River, Delta , Ebonyi Edo, Ekiti da kuma Enugu sun kada kuri'a.

13:57 'Yan majalisa daga jihohi 7 sun riga sun kamalla kada kuri'arsu inda ake takara tsakanin Hon Femi Gbajabiamila da kuma Hon Yakubu Dogara.

13:53 'Yan majalisar wakilai daga jihohi 36 da kuma Abuja su 360 za su zabi sabon kakakin majalisar.

13:40 'Yan majalisa daga jihohin Abia da Adamawa da kuma Akwa Ibom sun kada kuri'a.

13:17 Dan majalisa, Muhammed Sani Abdu daga jihar Bauchi ya gabatar da sunan Femi Gbajabiamila a matsayin dan takarar shugabancin majalisar wakilai.

Hakkin mallakar hoto Reuters

13:10 Dan majalisa, Abdulmumini Jibrin daga jihar Kano ya gabatar da sunan Mr Yakubu Dogara a matsayin dan takarar shugabancin majalisar wakilai

12:55 Akawun na kiran sunayen zababbun 'yan majalisar wakilai daya bayan daya.

12:25 Jami'an tsaron majalisar wakilai suna bi su tabbatar da cewa 'yan majalisa ne kawai ke zauna a kan kujerun majalisar. Saboda baki sun cika zauren, wasu zababbun 'yan majalisar ba suda wurin zama.

12:15 Akawun majalisar dokokin Nigeria, Alhaji Salisu Maikasuwa ya shiga majalisar wakilai domin gudanar da zaben shugaban majalisar.

Hakkin mallakar hoto NTA
Image caption Tsofaffin shugabannin majalisar wakilai, Ghali Umar Na'Abba da kuma Patricia Etteh

12:08 Jam'iyyar adawa ta PDP na da karfin fada a ji a sabuwar majalisar dattijai saboda Sanata Ekweremadu (Mataimakin shugaban majalisar) dan PDP ne.

12:05 An zabi Sanata Bukola Saraki ne a daidai lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya gayyaci 'yan jam'iyyar APC wata tattaunawa a dakin taro na International Conference Center da ke Abuja.

12:00 Sanata Ekweramadu ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattijai. Kenan ya yi tazarce saboda shi ne yayi mataimakin Sanata David Mark a majalisa a zango na bakwai.

Hakkin mallakar hoto NTA
Image caption Sanata Ekweremadu na shan rantsuwa

11:57 Sanata Muhammed Ali Ndume ya samu kuri'u 20 a yayinda Sanata Ike Ekwermadu 54. Sanatoci 75 ne suka kada kuri'a.

11:55 Sanata Ike Ekweremadu na jam'iyyar PDP ya zama mataimakin shugaban majalisar dattijai.

11:48 An kamalla zaben mataimakin shugaban majalisar dattijai. Ana kidaya kuri'un da sanatoci suka kada.

11:07 Ana ci gaba da kada kuri'a a zaben mataimakin shugaban majalisar dattijai tsakanin Sanata Ndume da kuma Sanata Ekweremadu. Ana kira sanatoci daya bayan daya. An soma daga jihar Abia.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bukola Saraki ya dare kujerar shugabancin majalisar dattawa

10:52 An soma gudanar da zaben mataimakin shugaban majalisar dattijai.

10:50 An gabatar da sunayen Sanata Ike Ekweremadu daga jihar Enugu da kuma Sanata Muhammed Ali Ndume daga jihar Borno domin takarar mataimakin shugaban majalisar dattijai.

10:45 Sanata Saraki ya zama shugaba ba tare da hammaya ba a majalisar dattijai.

10:43: An zabi, Sanata Bukola Saraki daga jihar Kwara a matsayin sabon shugaban majalisar dattijan Nigeria. Sanata Ahmed Sani ne ya gabatar da shi a matsayin dan takara.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sanata Bukola Saraki na shan rantsuwa

10:40 A majalisar wakilai kuma Femi Gbajabiamila daga mazabar Surelere a jihar Lagos ne zai fafata da Yakubu Dogora daga mazabar Tafawa Balewa da Bogoro a jihar Bauchi.

10:35 A majalisar dattawa manyan 'yan takarar su ne Sanata Ahmed Lawan daga jihar Yobe wanda 'yan jam'iyyar APC suka zaba a makon da ya gabata. Da kuma Sanata Bukola Saraki.

10:25 Jam'iyyar adawa watau PDP ta yi kira ga 'ya'yanta a majalisar dattawa su zabi tsohon gwamnan jihar Kwara Bukola Saraki a matsayin shugaba da kuma Mr Yakubu Dogara a majalisar wakilai.

10:20 Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya kira taro tare da 'yan majalisun dattawa da na wakilan kasar na jam'iyya APC dakin taro na International Conference center a Abuja da karfe 10 na safe. Amma ba a soma taron a kan lokaci ba.