Ku zabi Bukola da Dogara — PDP

Image caption Jam'iyyar PDP ta marawa Bukola da Dogara baya

Jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP ta yi kira ga 'ya'yanta a majalisun dattawa da na wakilai da su mara wa tsohon gwamnan jihar Kwara Bukola Saraki da Yakubu Dogara baya.

A wata sanarwa da sakataren jam'iyyar ta PDP, Olise Metuh, ya fitar jam'iyyar ta umarci 'yan majalisun da su tabbata sun bi umarnin da uwar jam'iyyar ta ba su.

Hakan dai ya biyo bayan takaddamar da ta dabaibaye zaben shugabannin guda biyu, a inda jam'iyyar APC mai mulki ta fitar da Sanata Ahmed Lawal a matsayin wanda zai yi takarar neman kujerar shugaban majalisar dattawa, sannan kuma jam'iyyar ta fitar da Femi Gbajabiamila a matsayin wanda zai takarar neman shugabancin majalisar wakilai.

Wasu dai na ganin matakin da jam'iyyar PDP ta dauka a matsayin wani yunkurin kara girman barakar da ke tsakanin 'yan jam'iyyar APC a majalisun biyu.