Wayar salula na haddasa faduwar dalibai

Wayar Salula Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Wayar Salula

Wani bincike da masana suka gudanar a Amurka ya nuna cewar dalibai ba za su dauki karatu ba sosai a kawunansu a yayinda suke karatun suna duba sakonni ko kuma aikewa da sakonni ta wayar salular su.

Masu binciken sun gano cewar dalibai wadanda ke karatun sakonni ko kuma aikewa da sakonni ta wayar su a yayinda suke nazari, ba su cika haye jarrabawa ba, kuma ma wurin daukar darasin suna zamowa koma-baya.

Nazarin ya gano yadda gungun wasu masu mu'amalla da wayoyinsu ke haduwa da wasu abubuwan a yayinda suke kokarin duba sako ko kuma rubuta sakonnin ta waya.

Masu binciken sun gano cewar lokacinda dalibai ba su amfani da wayoyin su, sun fi maida hankali da kuma tunano wasu bayanai.

Yayinda ake gab da fara jarrabawar dalibai, masu binciken a jami'ar Ohio da Nebraska za su kara shawartar iyaye da 'yan uwa su kara a muharar su, ko matasa za su iya daukar darussa a yayinda kuma a daya gefen sun karkata hankalinsu ga latse-latsen hanyoyin sadarwar su na zamani.

Masu binciken sun yi nazari a kan masu amfani da wayoyinsu na salula a cikin aji.

Lokacinda suka duba tasirin da aikewa da sakonni ta wayar da twitter ya haifar ga dalibai 145.

Binciken dai yana so ne ya gano ko matasa za su iya kansu biyu kamar dauka darussa suna rubutu a wani abinda ake koya musu ta hoton video suna rubutu kuma suna amsa tambayoyi, yayinda kuma a daya gefen suke fama da kutse a shafin na internet da suka shiga da woyinsu.

A tsakanin daliban jami'oi, binciken ya gano cewar, dalibai suna yawan amfani da wayoyi a cikin aji da kuma lokacinda suke nazari a gidajensu.

Karin bayani