Za a yi wa Boko Haram taron dangi

Sojojin Nijeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin Nijeriya

Hafsoshin sojin Nijeriya da na makwabta kasar za su gana a Abuja ranar Talata domin bullo da dabarun yaki da Boko Haram.

Wannan dai shi ne taro irinsa na farko za sojin na kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi za su gudanar tun bayan zaben Shugaba Muhammadu Buhari.

Hakan na zuwa ne bayan ziyarar da ya Shugaba Buhari ya kai kasar Jamus domin tattauna wa da kungiyar kasashen G7 kan yadda za a taimaka Najeriya.

Wani wakilin BBC ya ce muddin ana son cimma nasara a yaki da kungiyar ta Boko Haram, dole sai Najeriya ta hada karfi da kasashe masu makwabtakata da ita.

Karin bayani