Dashen jakar kwan mahaifa a Belgium

Kwan mahaifa Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption An cire jakar kwan mahaifar matar tun tana karama

Wata mata 'yar kasar Belgium ta zama ta farko a duniya da ta haihu ta hanyar dashen jakar kwan-mahaifa da aka cire mata tun tana karama.

Matar mai shekaru 27 wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta kaura daga Jamhuriyar Dimokradiyar Congo zuwa kasar ta Belgium, kuma an gano tana dauke da cutar amosanin jini ne ko kuma 'sickle-cell'' tun tana da shekaru 5.

Likitocin sun bukataci yi mata dashen bargo ne da aka kalato daga jikin wani dan uwanta saboda tsananin da cutar ta yi,

Kasancewar magugunan sanyaya kwayoyin halittar da aka bata ka iya yin nakasu ga kwayayen mahaifar ne yasa likitocin suka cire jakar kwan mahaifarta ta hannun dama tun tana da shekaru 13

'Firji'

Sun kuma adana jakar kwan mahaifar da ne a cikin Firji

Image caption Masana kimiyya sun shafe lokaci mai tsawo suna bincike

Shekaru 10 bayan yi mata aikin ne da ta bukaci samun haihuwa, likitocin suka sake dasa mata ajiyayyiyar jakar kwan da ke adane a cikin firji, inda aka samu nasarar ta samu juna biyu.

Ta haifi lafiyayyen yaro a cikin watan Nuwambar shekara ta 2014, amma kuma sai a yau din aka wallafa cikakkun bayanai game da batun a wata mujallar da hayayyafa a tsakanan al'umma

Likitoci sun ce wannan babbar nasara ce da za ta kwadaita fatan samun haihuwa a zukatan Mata da dama da suka hadu da larurar rashin haihuwa bayan sun yi fama da jinyar wasu cututtuka, ciki har da cutar Sankara ko Cancer.

A baya dai an jarraba amfani da jakar kwan-mahaifa ta manyan mata, kuma an dace, amma wannan ne karon farko da aka jarraba amfani da jakar kwan yarinyar da ba ta kai misali.