Goggon biri da shan barasa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Goggon biri ya fi kowane dabba dangantaka da mutum, kuma kamar mutum; shi ma yana shan barasa.

Goggon birrai sun nuna a baya suna fahimtar harshe, da sanin ya kamata, amma yanzu an gano dabban wanda da ya fi kowanne dangantaka da mutum, shi ma yana shan barasa.

Masana kimiyya da ke bincike a kan Goggon biri a kasar Guinea sun ga alamun sinadarin ethanol da ya shaida shan barasa na tsawon lokaci.

Binciken da aka dauki tsawon shekaru 17 ana yi, ya nuna Birrai na shan ganyen bishiyar barasar ne inda wasu ta ke kai su ga halin maye.

Wani bincike da aka wallafa a mujallar 'Royal Society Open Science' ya nuna bishiyar giyar da ta fi tsumuwa ce ta fi farin jini wurin birran.

Wasu mutane na tatsar bishiyar giyan a garin Bossou na kasar Guinea inda aka yi binciken, kuma su cika robobi safe da yamma, yayinda masu bincike kuma ke lura da birran suma suna shan na su a kan bishiyar.

'Binciken Masana'

Dr. Kimberely Hockings daga jami'ar Oxford Brookes da kuma cibiyar bincike a kan mutane a Portugal, wacce ke jagorancin tawagar binciken ta gano bishiyar giyan na da sinadarin 'alcohol' watau giya, kashi ukku cikin dari.

Likitar ta sheda wa BBC cewa "Birran na shiga yanayin maye, yayinda suke bacci cikin dan kankanin lokaci bayan sun sha, wani cikin su kuwa ya kasa sukuni sai tsalle-tsalle ya ke tayi, duk dai hasashe ne ba a tabbatar ba."

Giya tana da illa, amma ba a tabbatar da illarta ba ga dabbobin daji domin wannan shi ne karo na farko da aka yi binciken sa a birrai.

Hakkin mallakar hoto GOHASHI
Image caption Birran na amfani da gayan bishiyar giya wanda ke kama da soso, a shan barasar.

A da bincike ya nuna dabbobi da mutane na da son barasa, amma kuma wani sabon bincike da Mathew Carrigan na makarantar 'Santa Fe' da ke Amurka ya yi, ya nuna mutane da kuma birran Afrika na da wasu kwayoyin halitta a jikinsu da ke taimakawa masu wurin sarrafa sinadarin Ethanol.

Shi kuma Dr. Hobaiter daga jami'ar St. Andrews, ya ce "Gaskiya mun yi shekaru 60 muna bincike a kan Goggon biri, amma kullum mamaki suke bamu."