Sabuwar hanyar bunkasa cinikayya a Afrika

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Za a bude sabon yankin cinikayya a Afrika

Za a kafa sabon yankin cinikayya wanda zai zama mafi girma a Afirka, zai shafi kasashe 26 kuma zai hada da sama da mutane miliyan 600.

Yarjejeniyar, wacce za a sa wa hannu a Masar, na neman samar da sauki a wajen shigar da kuma fitar da kaya a kasashe mambobin kungiyar, wandanda ke samar da fiye da rabin na kudin shigar nahiyar Afirka a duk shekara.

Tun lokacin da aka kawo karshen mulkin mallaka na turawa, gwamnatoci suke tattaunawa a kan hanyoyi da za su bunkasa cinikayya a tsakanin kasashen Afirka.

Rashin kyawun tituna da hanyoyin jiragen kasa da kuma kamfanoni jiragen sama na kasashen sun sa ana fuskantar wahala wurin kai kaya zuwa kasashen da suke makwabtaka.

Tubalan cinikayyar su ne kungiyar kasashen kudancin Afrika SADC ; da kungiyar kasashen gabashin Afrika EAC da kuma kungiyar COMESA.