An kwaso gawarwakin 'yan Jamus zuwa gida

Adduo'i ga mutanen da suka mutu a hadarin jirgin Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Adduo'i ga mutanen da suka mutu a hadarin jirgin

An kwashi gawarwaki kashin farko na mutanen da suka mutu a hadarin jirgin saman nan na Jamus Germanwings zuwa kasar ta Jamus.

Mutane dari da hamsin ne suka mutu a cikin watan Maris lokacinda mataimakin matukin jirgin saman Andreas Lubitz ya fadi da jirgin saman na Fasinja a wurin shakatawar nan na Faransa watau French Alps.

Gawarwakin dalibai 'yan makaranta 16 na daga cikin mutane arba'in da 4 wadanda tun farko aka kwaso gawarwakinsu.

Danginsu dai za su samu damar ganin akwatunan gawar ta su a filin jirgin sama na Dusseldorf.

Karin bayani