An yi baran-baran a majalisar dattawa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sabon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki

An tashi baran-baran a zauren majalisar dattawan Najeriya tsakanin 'yan majalisar nan 53 da aka yi zaben shugabannin majalisar basa nan, da kuma sauran 'yan majalisar masu biyayya ga jagorancin shugaban majalisar Sanata Bukola Saraki.

Wannan dai ya biyo bayan kin sauraron bukatarsu ta a soke zaben da ya dora Bukola Sarakin kan kujerar shugaban majalisar da aka yi a ranar Talata.

Daga bisani 'yan majalisar, karkashin inuwar kungiyarsu ta Unity Forum, sun kira wani taron manema labarai inda suka yi watsi da zaben kuma suka ce za su kalubalance shi har a kotu.

Hujjojin da 'yan majalisar suka gabatar ta neman a soke zaben dai sun hada da cewa ya saba wa kundin tsarin mulki domin an take musu hakkinsu na shiga zaben wadanda za su shugabannin su.

Kuma acewarsu, akawun majalisar ya gudanar da zaben ne alhali yana sane cewa ba a samu adadin yawan 'yan majalisar da ka iya zaben shugabannin ba ko da sauran ba sa nan wato Quorum''.

A kan hakane 'yan majalisar karkashin jagorancin Senata Barnabas Gemade suka lashi takobin kalubalantar shugabancin Bukola Saraki.