Za a duba albashin 'yan siyasar Nigeria

Image caption Shugaba Buhari ya sha alwashin rage kashe kudaden gwamnati ba bisa ka'ida ba.

Hukumar da ke sa ido kan kayyade albashin manyan jami'an gwamnati ta fara wani yunkuri na sake duba dokar yadda ake biyan albashin masu rike da mukaman siyasa da ma'aikatan gwamnati da kuma alkalai ta 2008.

Shugaban hukumar Mista Elias Mbam ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, yayin da yake rantsar da mambobin kwamitin kayyade albashin wadanda za su yi aiki a kan sauya fasalin.

Mista Mbam ya bukaci kwamitin da ya rage irin yadda ake kashe kudin gwamnati, duba da halin ha'ula'in da tattalin arzikin kasar ya shiga.

Hakan ya biyo bayan karfin da kundin tsarin mulkin kasa ya bai wa hukumar ne domin ta tantance alawus-alawus na masu rike da mukaman siyasa.

Tuni dai shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci da a rage yawan kashe kudaden gwamnati ta hanyar da ba su dace ba.