An yi zaben majalisun Najeriya a kan tsari

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban majalisar dattawa a Najeriya, Bukola Saraki, a lokacin da ake rantsar da shi

Wani masanin kimiyyar siyasa a Najeriya, Dr. Kabir Mato wanda malami ne a sashen koyar da kimiyyar siyasa a jami'ar Abuja, babban birni Najeriya ya ce zaben da aka yi a majalisar dokoki da ta wakilai bai saba kundin tsarin mulki ba.

Dr. Mato wanda ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da BBC, ya ce dokar tsarin majalisun biyu sun bai wa 'yan majalisar dama na zaben mutanen da suke son su jagorance su da kansu.

Dangane kuma da bijirewa umarnin jam'iyyarsu ta APC da wasu 'yan majalisun suka yi, Kabir Mato ya ce hakan ya dace domin ita jam'iyyar tana neman yi wa 'ya'yan nata karantsaye a kan hurumin da ba nata ba.

Duk da cewa masanin kimiyyar siyasar ya amince da cewa tirka-tirkar ta kara haskaka tsarin dimokradiyyar Najeriya amma ya ja hankali jam'iyyu da su shiga taitayinsu domin ka da irin haka ta kara faruwa a nan gaba.