Sudan ta Kudu na fuskantar yunwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Salva Kiir da Reik MAchar shugaban 'yan adawa

Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta yi gargadin cewa dubun-dubatar mutane na fuskantar barazanar yunwa a Sudan ta Kudu, inda fada ya yi kamari tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye.

Kungiyar Red Cross ta ce akwai bukatar bangarorin biyu da kungiyoyin bayar da agaji da kuma gwamnatocin kasashen waje su dauki matakan gaggawa kuma masu dorewa.

An kiyasta cewa kimanin mutane miliyan biyu ne suka kauracewa muhallansu tun lokacin da aka fara rikici a Sudan ta kudu, watanni 18 da suka gabata.

Kungiyar ta kuma ce amfanin gona suna rubewa a gonaki kuma kungiyoyin sojojin sa kai suna sace dabbobi da abinci.