Boko Haram: Amurka za ta ba da tallafi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Barrack Obama na Amurka

Gwamnatin Amurka za ta bayar da gudunmawar dala fiye da miliyan 10 domin taimakawa mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa a arewa maso-gabashin Najeriya.

Amurkar za ta mika tallafin kudaden ne, ga hukumar lafiya ta duniya WHO da UNICEF da kuma hukumar da ke sa ido kan yawan al'umma na majalisar wadanda za su aiwatar da ayyuka a jihohi uku da rikicin Boko Haram ya fi shafa a Najeriyar.

Za a yi amfani da kudaden ne wajen samar da abinci mai gina jiki ga kananan yaran da ke fama da tamowa da inganta harkar kiwon a sansanonin 'yan gudun hijira inda wadanda rikicin boko haram ya daidaita ke zaune a arewa maso gabashin Najeriya.

Kimanin mutane miliyan daya da rabi ne dai rikicin na Boko Haram ya raba da matsugunasu a kasar ta Najeriya.

Rikicin kuma ya janyo mutuwar mutane kusan 15,000 cikin shekaru shida.