Za a kori masu tallafa wa IS daga Australia

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Firaiministan kasar Australiya, Tony Abott da matarsa

Firai ministan kasar Australia,Tony Abott, ya sha alwashin kwace lasisin duk wani dan kasar mai ruwa-biyu wanda kuma aka same shi da laifin taimakawa 'yan kungiyar IS.

An dai hakikance cewa kimanin 'yan kasar 100 suna kasashen Iraq da Syria suna taya IS yaki.

Kasar ta Australiya ta kudiri dakile shirin kungiyar IS na jan ra'ayin mutane da su yi jihadi ta kafar intanet.

A wani taron kolin kasashen yankin Asiya da Pacific wanda kasashe 25 suka halarta, Tony Abott ya yi kira da su hada karfi da karfe wajen taimakawa a yaki kungiyar IS a duniya.