Za mu murkushe mayakan IS a Iraqi - Amurka

Mayakan Kungiyar Islamic Jihad Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Mayakan Kungiyar Islamic Jihad

Prime Ministan Australia Tony Abbott ya yi kira ga kasashen yankin Asia da Pacific su hada karfi don taimakawa a yaki kungiyoyin masu jihadi.

Ya gaya ma Ministoci daga kasashe ashirin da biyar a taron da ake yi kan sha'anin tsaro a yankin a birnin Sydney cewar kungiyar IS mai da'awar kafa kasar musulunci tana da wani guuri na mamaye duniya, yana cewar kungiyar makasa ce mai rassa da dama.

Yana magana ne jim kadan bayan Shugaba Obama ya amince da shirin tura karin wasu mayakan Amurka dari hudu da hamsin zuwa lardin Anbar na Iraqi wurinda mayakan na kungiyar IS suka samu gagarumar galaba.

Karin bayani