Bam ya kashe wasu sojojin Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ba a san wanda ya dasa rokar a cikin motar ba.

Rahotanni daga lardin arewa mai nisa na kasar Kamaru na cewa sojojin kasar biyu sun mutu sakamakon fashewar wata roka a cikin motar da ta dauke su.

Wakilin BBC ya ce lamarin ya faru ne a garin Bodo da yake yankin Logone da Chari na lardin arewa mai nisa.

Wakilin namu ya kara da cewa baya ga sojoji 23 sun samu rauni sakamakon lamarin.

Har yanzu dai ba a san wannan ya dasa rokar a cikin motar ba, sai dai kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare a kasar.