Cutar Ebola na sake yaduwa a Guinea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cutar Ebola na sake yaduwa a Guinea da Saliyo

Hukumar lafiya ta duniya ta ce an samu karuwar wadanda suka kamu da cutar Ebola a kasashen Guinea da Saliyo cikin makonni uku a jere.

Mai aikowa BBC rahotanni kan harkar lafiya ya ce an kuma samu yaduwar cutar a wasu yankuna da dama fiye da makonnin da suka gabata.

Masu bincike sun gano cewa hanyar da ake bi wajen yin jana'iza ba tare da daukar matakin kariya ba shi ne babban abin da ke jawo kara yaduwar cutar a Guinea.

Tun kimanin wata guda da ya gabata ne kasar Laberiya ta fita daga sahun kasashe masu fama da cutar ta Ebola.