'Yan gudun hijirar Boko Haram za su samu taimakon Amurka

'Yan gudun hijirar Boko Haram
Image caption 'Yan gudun hijirar Boko Haram

Gwamnatin Amurka ta ce za ta bayar da karin gudunmawar dala fiye da miliyan10 domin taimakawa mutanen da rikicin Boko Haram din ya shafa a arewa maso-gabacin Najeriya.

Amurkar za ta mika tallafin kudaden ne ga hukumar lafiya ta duniya WHO da asusun tallafawa kananan yara na Majalisar dinkin duniya, UNICEF da kuma hukumar da ke sa ido kan yawan al'umma na majalisar wadanda za su aiwatar da ayyuka a jihohin Uku da rikicin Boko Haram ya fi shafa a Najeriyar.

Mutane kimanin miliyan daya da rabi ne dai rikicin na Boko Haram ya raba da matsugunansu a Najeriyar.

An yi bikin sanya hannu kan yarjejeniyar ba da kudin yau a ofishin jakadancin Amurkar da ke Abuja .