Boko Haram: Kasashen tafkin Chadi na taro

Hakkin mallakar hoto BOKO HARAM
Image caption Taron dai zai mayar da hankali kan yadda za a magance matsalar Boko Haram

Shugabannin kasashen da ke makwabtaka da Tafkin Chadi da kuma Jamhuriyar Benin, za su gana a Abuja, birnin tarayyar Najeriya, ranar Alhamis da nufin daukar muhimman matakai na kafa rundunar hadin gwiwar da za ta yaki kungiyar Boko Haram.

Kasashen dai sun hada da Najeriya da Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Nijar da Benin.

Wannan taro dai na zuwa ne bayan tarukan da manyan hafsoshin sojin kasashen suka yi ranar Talata da wanda ministocin tsaronsu suka yi ranar Laraba, inda suka shata wasu manufofi na tabbatar da nasarar yaki da ta'addanci.

Tuni dai shugabannin suka umarci Hukumar Raya Tafkin Chadi ta bullo da wani shiri na samar wa matasa ayyukan yi da nufin taimakawa wajen rage talauci a yankin arewa maso gabashin Najeriya da kuma sauran yankunan da tashe-tashen hankula na mayakan kungiyar Boko Haram suka lalata.