'Aliyu ya ranci naira biliyan uku a Niger'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsohon gwamnan jihar Niger, Mu'azu Babangida Aliyu

Gwamnan jihar Niger, Alhaji Abubakar Sani Bello ya bukaci jami'an tsohuwar gwamnatin jihar, su mayar da kudaden gwamnati da suka barnatar.

Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Dr Ibraheem Dooba ya sanya wa hannu, ta ce jami'an tsohuwar gwamnantin karkashin jagorancin Mu'azu Babangida Aliyu su mayar da naira biliyan biyu da miliyan dari tara da suka kwashe.

Dooba ya ce "Sun karbi bashin gwamnati kwana daya kafin wa'adin mulkinsu ya kare, sannan suka raba a tsakaninsu."

"Alal misali a ofishin sakataren gwamnati an karbi naira miliyan 600 kuma ba a bayyana abin da za a yi da kudin ba," in ji kakakin sabon gwamna.

Gwamna Bello ya ce ba shi da niyar yi wa tsohuwar gwamnatin jihar bi-ta-da-kulli amma kuma babu yanda za a yi a kawar da kai daga wurin wadanda suka sace kudin gwamnati.

Kakakin tsohon gwamna Mu'azu Aliyu wato Israel Ebije ya ce babu ko asi da gwamnatinsa ta kwashe.