Australia na tasa keyar 'yan ci-rani

Masu neman mafaka daga Indonesia Hakkin mallakar hoto AFP GETTY IMAGES
Image caption Masu neman mafaka daga Indonesia

Prime Ministan Australia Tony Abbott ya ki ya musanta rahotannin da ake bayarwa cewar jami'ai masu tsaron kan iyakar kasar suna biyan kudi ga mutane masu fasa-kwouri suna tasa-keyar jiragen ruwa dake makare da masu neman mafaka daga Indonesia zuwa wurinda suka fito.

Lokacinda yake maida martani ga ikirarin da wani jami'in 'yan sandan Indonesia ya yi cewar jami'an Australia sun biya dala dubu talatin ga masu fasa-kwourin mutanen, Mr Abbott ya ce, "ana amfani da wasu hanyoyi da aka kirkiro" na hana jiragen 'yan ci-ranin shiga kasar.

Wakilin BBC a Sydney ya ce Australia ta dauki tsattsauran mataki a kan masu neman mafaka, tana kuma samun nasarar hana jiragen ruwan isa gabar ruwan kasar ta.

Karin bayani