Jamus za ta gina gidaje don 'yan gudun hijira

Image caption Yawan 'yan gudun hijira na karuwa a Turai

Jamus ta amince za ta kashe fiye da euro biliyan daya a bana domin gina gidaje saboda karuwar 'yan gudun hijira a kasar.

An kiyasta cewa kimanin mutane 400,000 ne za su nemi mafaka a Jamus a bana, yawan da ya haura adadin na bara.

Ana ci gaba da hurawa gwamnati wuta domin ta kara samar da kudade domin taimakawa garuruwa da biranen da ke kokarin shawo kan cunkoson.

Jamus tana karbar bakuncin 'yan gudun hijira fiye da kowacce kasa ta kungiyar tarayyar Turai.

Tana kuma yin kira ga sauran kasashe da su dinga karbar bakuncin 'yan gudun hijira masu yawa.