Za mu yi maganin Boko Haram — Sojoji

Hakkin mallakar hoto nigeria defence forces
Image caption Sojojin Najeriya suna tsimar yaki

Sojojin Najeriya masu yaki da kungiyar Boko Haram a jihohin Borno da Adamawa sun sha alwashin karya lagon 'yan kungiyar.

Wannan alwashin ya biyo bayan wata ziyarar karfafa gwiwa da babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya, Laftanar Janar Kenneth Minimah, ya kai rundunonin sojoji masu yaki da kungiyar a jihohin Borno da Adamawa.

Mai magana da yawun sojojin kasar, Kanal Usman Kuku-Sheka, wanda ya yi wa babban hafsan rakiya, ya ce sojojin sun tsumu da kalaman da Kenneth Minimah ya fada musu dangane da kudirin gwamnati na biya musu duk abubuwan da suke bukata domin yin yaki.

Sai dai wasu na yi wa ziyarar kallon wani sabon al'amari a karkashin wannan gwamnati amma mai magana da yawun sojojin ya ce da ma can ana irin wannan ziyara illa iyaka mutane ba su sani ba ne.