Sarki Sanusi ya zama shugaban Rhino

Image caption Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu

Kamfanin makamashi na Rhino ya bai wa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu mukamin shugaban hukumar daraktocinsa.

A watan Janairun 2012 ne aka bude kamfanin makamashi na Rhino domin inganta harkar zuba jari a harkar samar da wuta da jigilar man fetur a nahiyar Afrika.

Shugaban kamfanin Brian Herlihy, ya ce "Wannan wani babban ci gaba ne ga hukumar daraktocin kamfanin Rhino. Kuma Sarkin ya san irin ci gaban da tattalin arzikin Afrika ke bukata da kuma rawar da bangaren wutar lantarki za ta taka."

Mista Herliy ya kuma kara da cewa "mun yi amanna cewa a matsayin shugaban daraktocin Rhino, Sarki Sunusi zai dinga bayar da shawarwari kan yadda za a inganta kasuwanci a nahiyar Afrika baki daya."

Sarki Muhammadu Sanusi na biyu shi ne tsohon gwamnan babban bankin Nigeria, wanda kuma ya shafe shekaru 25 yana aikin banki a kasar kafin ya hau gadon sarautar Kano.